Advertisement

Shahararren mawakin Nijeriya ya rasa danshi

Rahotanni sun bayyana cewa mawakin yana birnin Los angeles a Amurka domin halartar bikin karrama fitattun na BET sanda wannan mummunar labarin ya iso ma kunnen shi.
Advertisement

Shahhararren mawakin nan mai tauraro, Dbanj yana jimamin rasuwar dan  shi mai shekara 1.

Advertisement

An samu labari cewa dan mai suna, Daniel Oyebanjo na uku, ya mutu ne sanadiyar nitsewa a cikin ruwan ninkaya dake nan gidansu a unguwar Ikoyi dake jihar Legas.

Yaron dai ya rasu bayan yan kwanaki da yin bikin zagayowar haihuwar sa na cika shekara daya a duniya.

Sai dai D'banj bai tabbatar da labarin ba amma ya saka wani bakin hoto a shafin sa na kafar sada zumunta inda ya rubuta "Wannan lokacin ne na jarabta, kuma na yi imani da hukunci ubangiji".

Rahotanni sun bayyana cewa mawakin yana birnin Los angeles a Amurka domin halartar bikin karrama fitattun na BET sanda wannan mummunar labarin ya iso ma kunnen shi.

Advertisement

KAmar dai yadda rahotanni suka bayyana, an kai gawar yaron zuwa dakin ajiyar matatu dake nan Ikeja.

Game da rashin dai mutane da dama masu hannu da shuni a fannoni daban daban da dinbim masoyai sa sun taya shi jaje game da rashin.

Shima dan majalisar dattawa, Sen Murray Bruce, ya mika sakon ta'aziya ga iyalen mawakin.

Hakazalika abokan aiki sa da saura masu taka rawar gani a dandalin  nishadi sun taya shi jaje.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement