ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yar kunar bakin wake ta kai hari masallaci a garin Fulatari

lamarin ya faru ne ranar 2 ga wata da misalin karfe 5:30 na safe yayin da ake sallar asuba. Mutum biyu sun jikkata sakamakon fashewar bakin waken wanda ya kashe ita mai kokarin aiwatar da mummanar harin.

Kamar yadda wani shaidar gani da ido ya sanar, macen mai dauke da bom tayi yunkurin shiga cikin masallaci ne domin tayar da ita sai bata samu nasara ba inda wani daga cikin masallatar masallacin ya dakatar da ita.

Cikin kokarin hana ta shiga bom din ya fashe. jim kadan bayan fashewar bakin waken sojoji suka halarci wajen inda suka tafi da wadanda suka jikkata asibiti dake Damaturu.

Kwamishnan yan sanda na jihar Abdulmalik Sunmonu ya tabbatar da faruwar hakan inda ya kara da cewa jami'an sa sun sanar dashi game da harin.

Malam Baana Isah mazaunin garin yace tarzomar da harin ya haifar yasa an rufe makarantu da kasuwanni har sai al'ummar garin sun samu tabbacin tsaro daga jami'o'in tsaro.

ADVERTISEMENT

Wannan shine karo na farko bayan makamancin harin da ya faru a yankin tun watan afrilu na 2016. Al'ummar yankin sun samu sukuni bisa aikin da sojoji keyi wajen kawar da yan ta'adda da aikin ta'adanci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT