ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wani magidanci ya gamu da fushin uwardakin shi, ta watsa masa ruwan batiri a gaba

Ta zuba masa ruwan batiri a gaban shi yayin da yake bacci wanda yayi sanadiyar mutuwar shi bisa dalilin yi ma aminiyarta ciki

Uwardakin ta aikata hakan ne bayan ta tarbe mijinta hannu biyu bayan dawowar shi daga wani dan gajeren tafiya da yayi. Cikin rarrashi ita da mijin nata sunyi kwanciyar ma'aurata sai dai bayan kwantatawan da ta nuna mashi can cikin dare ta aikata mummunar aikin wanda yayi sanadiyar mutuwar sa.

Kamar yadda labari ya zo mana matar wanda ta aikata laifin ta samu ruwan batirin daga wani mai gyaran mota mai suna Kabir.

Makwabta suka yi gaggawar kai mijin asibiti da ke kusa da su amma sai ma'aikatan asibitin suka ki karbansa suka tura su zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya da ke nan Zaria.Bayan an kwantar da shi a asibitin, a ranar 20 ga watan febreru Allah Ya yi masa cikawa.

Rundunar yan sanda na jihar Kaduna sun bayyana cewa sun kama matar tare da Malam Kabir da ya sayar mata da ruwan batir din.

ADVERTISEMENT

Uwargidan tayi naddamar laifin da ta aikata wa mijin nat\a wanda ya kai har ga mutuwar shi.

Tana mai cewa "Ina kaunar mijina sosai kuma banyi niyar kashi ba. Nayi bakin cikin jin labari cewa yayi ma aminiyata ciki kuma bai sanar dani ba. Daga majiya na samu wannan labarin.

"Na san na wuce gona da iri amma ina rokon yan uwanshi da yara na har da gwamnati da su yafe mun. Banyi niyar kashi ba" Ta kara.

Rundunar yan sanda sun ce zasu mika su gaban kotu bayan kammala bincike kan lamarin domin fuskantar hukuncin laifin da ta aikata.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT