Shanu ya hana Jirgin Sama saukowa
Ɗaya daga cikin fasinjojin wannan jirgi Mr Richard, ya bada labari cewa wannan faruwa ya hana jirgi saukowa.
Bayan sun yi santa na kusan minti talatin a sama, masu kula da zirga-zirga na jiragen sama sun bada damar sauka. Fasinjoji sun tsorata sossai, kuma sun gigice.
Da farko, fasinjoji basu san dalilin da ya hana matuƙi daga saukowa ƙasa.
Sun ci gaba da gunaguni da kuma zargin matuƙi. Amma, bayan Allah ya ƙaɗaraʼd da saukan lafiya, matuƙi ya bayyana abinda yake faruwa a ƙasa.
Daga baya, fasinjoji sun yaba masa, kuma sun yi masa godiya domin matakin da ya ɗauka.
Wannan ba shine farko ba ga irin wannan aukuwar a filin jirgi. A titin jirgi na Port Hacourt, makiyayan shanu sun kori shanunsu akan filin jirgin sama, har ma shanu sun hau kan titin jirgi.
Sai wani Jirgin sama na kamfanin Air France sun yi karo da dabbobi masu yawa.
Idan ba da ƙaddaran Allah, mutane da dama sun rasa rayuwarsu. Jirgin Air France ta lalace sossai kuma fasinjoji sun gigice.
A takaice, gwanatin Najeriya ta ɗauki nauyin gyara na wannan jirgi.
Da muka nemi Manajan kamfanin Air Peace akan wayan tarfon, babu wanda ya ɗauki waya.
Muna koƙarin samun su ga waya domin mu kawo muku cikaken labari na wannan faruwa.