Advertisement

Masu fashi da makamai sún kai ma bankuna biyu hari. Sun kashe Manaja da mutane ukku

Muna da labari cewa ʼyan sanda sun tsere daga kewayen bankuna a lokacin da masu fashi sun kai hari.
Advertisement

Muna da rahoto cewa a lokacin da aka kai wannan hari cikin ƙaramin hukumar Otun-Ekiti, ʼyan sanda wanda ke kusa, sun tsere da gudu.

Advertisement

Bayan an yi lissafi, Manajan Banki, kashiya, wani maʼaikacin banki da kuma mai gadin gidan Sarkin gari, duka sun rasa rayuwansu.

Muna da labari cêwa ɗaya daga cikin mai-gadin Sarkin gari yana shirin bikin aurenʼ sa a lokacin da wannan hari ya taso.

Da yáke bayani, Sarkin Gari mai suna Adedapo Popoola, ya faɗa cewa masu fashi sun yi aikin hari na tsáwon  saʼa guda cikin kwancen hankali, kuma ba tare da damuwa ba.

Sun yi halbe-halbe da bindiga, kuma sun sâki manyan nakiyoyi daban-daban.

Advertisement

Sarkin gari ya yi bayani kamar haka:

"A daidai ƙarfe shida na yamma, ina wajen hutawa a gaban fadar tare da ʼyan majalisa na gari. Sai muka ji wani babban ƙara mai iya fashe kunnuwa. Mun yi zarton céwa wataƙila wasu matasa suna wasan wuta (waton fireworks) domin yin bushara na bikin kirisimati."

"Amma can gaba, mun sake jin ƙara na fashewa masu yáwa, da kuma kamanin ƙárán bidiga. Sai muka yarda cewa lallai wanan masifa ya wuce wasan yará ko matàsá."

"Tashin ƙara na bindiga da ragargaza ya ci koʼina. Mun kasa fahimtar abinda yake faruwa. Mun yi tunani cewa, ko ʼYan Boko Haram sun shiga garinmu ne?  Na yi zabura domin in tsere, amma sai na rikice domin rashin sani hanya wanda zan bi."

"Daga baya, mun sanar da mu cêwa masu fáshi da makamai, sun kafa kansu a bakin kofofi guda huddu na  garinmu. Sun kafa wasu abokan aikinsu a hanya na Orimope kusa da offishin ƙaramin hukuma na Moba. Sun kafa kansu a gaban fadar Sarki da kuma gaban Koleji na fasaha wanda yake hanyar Kwara."

Advertisement

"Halbe-halbe da kuma ƙaran bam ya yi daɗewan saʼa guda. Kafin saukúwar ƙuran da aka táyar , mutum huɗu sun rasa rayuwarsu. "

Sarki ya bayyana cewa a lokacin da ake wannan tashin hankali, ya nemi gwamnan Jihar akan wayan tarfon.

Gwamna Ayodele Fayose, ya shirya masu tsaro a nan take zuwa cikin garinmu.

Amma kafin ʼyan tsaro su isa wurin tashin hankali, masu fashi sun kammala da aikinsu, kuma sun tsere.

Wakilin ʼyan sanda na Jihar Ekiti mai suna Mr. Alberto Adeyemi, ya tabbatar da wannan faruwa.

Advertisement
Advertisement
Latest Videos
Advertisement