Advertisement

Mahaifin shahararren mawakin arewa ya rasu

Mawakin ya sanar da labarin mutuwar mahaifin shi a shafin sa na kafafen sada zumunta.
Advertisement

Mahaifin shahararren mawakin gambara na arewa King Bawa wanda aka fi sani da Kheengz ya rasu.

Advertisement

Mawakin wanda ya shahara a fannin wakar hip-hop ya sanar da labarin rasuwar ne a shafin sa na dandalin sada zumunta.

Kamar yadda ya sanar mahaifin sa ya rasu ne ranar alhamis 13 ga watan Satumba.

Yana mai mika sakon godiyan sa ga dinbim masoya da suka taya shi jaje tare da yin kira ga sauran jama'a da su taimaka su cigaba da yi masa addua'a.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement