ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Saudiya na shirin karrama dan wasa da kyautar fili a Makka

Kamar yadda labarin ya fito, kasar zata karrama shi ne bisa gudumawar da ya bada wa wajen raya addinin musulunci

Dan wasan yana cigaba daga tutar Afirka a gasar firimiya, inda a halin yanzu ya saka kwallaye 43 a raga cikin wannan kakar da ake ciki wanda da hakan ya kafa tarihi a kungiyar Liverpool.

Wannan labarin kyauta ya fito ne a wata sanarwa da mataimakin shugaban kasar Makka, Fahd Al-Rowky, ya fitar ranar litinin 23 ga wata. Yace za'a karrama shi ne bisa kokarin da yayi na zama gwarzon dan wasa a Ingila.

Kamar yadda jaridar ta fitar, an baiwa dan wasan zabi tsakanin samun fili a Makka ko gina masallaci da sunan shi ko kuma a siyar da fili kana mika masa kudin.

Al-rowky ya bayyana cewa, idan har hukumomin kasar sun amince, za'a mallaka masa fili ko a zabi daya daga cikin zabin da suka fitar.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda labarin ya fito, kasar zata karrama shi ne bisa gudumawar da ya bada wa wajen raya addinin musulunci wanda a sanadiyar shi, wasu magoya bayan kungiyar Liverpool da masu bibiyan kwallon kafa ke sha'awar musulunci.

Wani dalilin karrama shi, shine ganin yadda yake taka rawar gani wajen aiwatar da ayyukan agaji ga mara sa galihu tare da taimakon da yake baiwa matasa na gina kansu.

Shi dai wasan, yana cigaba da samun jinjinawa daga dinbim hukumomi da masu bibiyan kwallon kafa bisa rawar da yake takawa a kakar bana ga tawagar sa Liverpool da ta kasar Egypt.

Mohammed Salah shine zakaran yan wasan nahiyar Afrika bana kuma shine wanda ya lashi kyautar gwarzon Ingila.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT