ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Daliban da aka saki sun koma ga iyayen su

A bisa labari da NAN ta ruwaito iyayen matan sun nuna farin cikin su bisa dawowar su inda suka tarbe su cikin murna da annashuwa

Mata 104 cikin su 110 aka mayar tare da wasu yara biyu.

Jim kadan bayan dawowar su an tafi da yan matan fadar shugaban kasa inda suka samu kulawa saanan suka gana da shugaban kasa.

Yan mata sun samu rakiya daga jami'an gwamnatin tarayya daga filin jirgi da suka sauka a Maiduguri zuwa garin Damaturu.

ADVERTISEMENT

A bisa labari da NAN ta ruwaito iyayen matan sun nuna farin cikin su bisa dawowar su inda suka tarbe su cikin murna da annashuwa.

Sai har yanzu iyayen daya tilo na daga cikin yan matan dake garkame har yanzu a hannun wadanda suka sace su suna bakin cikin rashin sakin diyar su.

Dalibar mai suna Leah Sharibu ita kadai ta rage a hannun su kuma a wata shaida da daya daga cikin sauran matan da aka saki tayi, an cigaba da tsaron ita Leah kasancewa taki amincewa wajen sauya adini zuwa ta musulunci.

Ganawan shi da yan matan a fadar sa, shugaba Buhari ya sha alwashin yin iya bakin kokarin shi domin ganin an sake ta.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT