ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Saudiyya na shirin hana yan Nijeriya zuwa aikin hajji bana

Musa Ubandawaki ya shaida cewa an gudanar da taro tsakanin jami'ai daga jihohi 36 na kasa da jami'an hukumar na tarayya domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan barazanar da Saudiyya ta yi wa kasar

Mai magana da yawun hukumar hajji na nijeriya, Musa Ubandawaki ya shaida hakan ne a taron da aka gudanar ranar laraba tsakanin, jami'ai daga jihohi 36 na kasa da jami'an hukumar na tarayya domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan barazanar da Saudiyya ta yi wa kasar.

A jawabin sa wajen taron, ministan lafiya kasar Farfesa Isaac Adewole, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bin matakan da ya kamata, don ganin an yi ingantaccen shirin da za a tabbatar don magance matsalar zazzabin Lassa a tsakanin maniyyata a kasar.

A Nijeriya akalla mutum 90 suka halaka sakamakon cutar yayin da fiye da mutum dubu daya suka kamu da cutar a sassa daban-daban na fadin kasar bana.

Kwayar cutar na bazuwa ne daga jikin wadanda suke cin berayen da ke dauke da kwayar cutar ko kuma abinci da ya hadu da kashi ko fitsarin bera.

ADVERTISEMENT

Hakazalika ana yiya kamuwa da cutar idan jinin wanda yake dauke da kwayar cutar ya hadu da wanda bashi da shi ita.

A cikin watan Agusta ne za'a fara aikin hajji na bana.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT