ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Bukola Saraki ya jagoranci sauran yan majalisar dattawa zuwa fadar shugaban kasa

A zaman da yan majalisar suka yi ranar talata 16 ga wata,sun bukaci babban sufeton yan sanda na kasa da ya kama wadanda suka gudanar da harin da ya faru a jihar Benuwe cikin kwana 14

Yan majalisar sun tattauna tare da shugaban kasa akan harkar tsaro dake fuskantar zagon kasa tare da mafita da za'a samad wajen kawar da rikicin makiyaya da manoma.

kafin zuwan su fadar shugaban, yan majalisar dattawa sun umarci babban sufeton yan sanda da ya kama wadanda ke da hannun a harin da ya faru a jihar Benuwe wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 73 cikin kwana 14.

A zaman da suka yi, yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin tarayya da dau kwakkwarar mataki akan wannan rikicin.

ADVERTISEMENT

Yayin da ya gana da manema labarai dake fadar shugaban kasa bayan tattaunawar da suka yi da shugaban, Saraki ya sanar cewa sun je ne domin zayyana ma shugaban kudurin da majalisar ta fitar a zaman su game da rikicin makiyaya.

Mai baiwa shugaban kasa Shawara a kan ayyukan majalisar dokoki Ita Enang ya jinjina ma yan majalisar bisa zaman da suka yi kan harkar tsaron kasa ba tare da an jingina ta da bambamcin akidar siyasa ko jam'iya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT