ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Maʼaikatan man fetur da iskar gas sun soma yajin aiki yanzu

Ƙungiyar maʼaikatan man fetur da iskar gas (waton NUPENG), ta soma yajin gama-gari saboda rashin-bin ƙaʼidan aiki da korar ʼƴaʼƴanta daga aiki.

Maʼaikatan man fetur da iskar gas sun soma yajin aiki yanzu

Ƙungiyar maʼaikatan man fetur da iskar gas (waton NUPENG), ta soma yajin gama-gari domin sanar da Gwamnati akan buƙatan da suke yi na gyaran ƙaʼidojin aiki a sashen masanaʼantun man fetur da iskar Gas.

Shugaban Ƙungiyar PENGASSAN, Achese Igwe, ya cê shuagabanin ƙungiya sun ɗauki matakin ne bayan gamuwan da suka yi a ranar Talata. Ya yi bayani cêwa wannan yajin aiki ya zama wajibi saboda kamfanonin man da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kan jin daɗin maʼaikata. A bayanin da yayi, za su tattauna da ministan ƙwadagon ƙasar Chris Ngige domin ya shiga tsakaninsu da kamfanonin man.

Wannan yajin-aiki dai zai yi tasiri wajen hako da fitar da man fetur da iskar gas. Ga kalaman shugaban Ƙungiyar NUPENG:

"Shuagabanin Kungiyar NUPENG sun yi taruwa domin sake nazari akan yajin aiki da aka shirya. Kamar yadda kuka sani, wannan yajin-aiki yana da tabbataccen ranar ƙarewa- waton bayan kwana uku.

ADVERTISEMENT

Mun ɗauki wannan mataki domin yin kwatancin muhimmacin matsalolin da muke fama da shi. Matsalilon sun shafi rashin tabbaccin aiki, rashin cika alkawarin yarjejeniya wanda aka shiga tare da masu ruwa da tsaki na sashen man fetur da iskar Gas a Ƙasar Najeriya gaba ɗaya, da kuma rushewa na gyaran ƙaʼidojin zuba jari a cikin tsarin kamfanonin man fetur da iskar Gas.

Shuagabani sun ba da umarni cêwa za mu ci gaba da soma yajin aiki na kwana uku har lokacin da za mu samu ƙarin umarni daga kwamitin na shuagabanin Man Fetur. Ministan kwadagon ƙasar ya kira Ministan Man Fetur domin tattaunawa akan waɗannan matsaloli. Muna fatar cêwa taruwansu zai warware alʼamuran da suka shafe mu. Idan sun kasa, za mu ci gaba da yajin aiki."

Kungiyoyin maʼaikatan man dai sun daɗe suna yajin-aiki a Najeriya, akasari domin su matsa a aiwatar da wasu matakai wanda suke son ganin an ɗauka.

Sai dai ʼƴan kasar da dama na ganin yajin-aiki ba shi ne mafita ba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT