Ga yanda manyan kulob na turai suka kakara a gasar zakarun turai jiya laraba 13 ga watan Satumba.
Yanda a tashi a wasannin Champions league jiya
Real madrid ta sharara kwallaye a raga, Stones yaci kwallo biyu, Liverpool tayi kunnen doki yayin da Tottenham ta ba Dortmund kashi
Real madrid tayi wa APOEL nicosia bugu a wasan da aka a filin santiago bernabeau. Zakaran Turai Cristiano Ronaldo ya gan bayan gola so biyu kuma mai tsaron baya watau Sergio Ramos yayi tattaki tun daga baya zuwa ragar APOEL har ma ya cinma burin sa inda ya sa kwallo ta uku a ragar abokan adawar su cikinwasan da Real ta lashe 3-0.
Manchester city na kasar Ingila ta ziyarci Fayenoord na kasar Holland har ma suka sharara masu kwallaye hudu a raga a babban filin De kuip. Mai tsaron bayan Man city John Stones ya ga bayan gola sau biyu yayin da Aguero da Gabriel Jesus suka nuna kwarewarsu suka sa kwallo daya-daya.
Liverpool tayi kunnen doki da Sevilla. Firmino da Sallah suka sanya kwallo a ragar Sevilla amma bai hana Yedder da Correa da su taimaka ma Sevilla a wasan da aka a filin Anfield. Abun bakin ciki da ya faru a wasan shine Firmino ya buga Finariti a turke cikin wasan da aka tashi 2-2.
A kakara da Tottenham tayi da Dortmund, tawagar kasar Ingila ta nuna kwarewa inda suka lashe Dortmund suka sa kwallo 3 uku a ragar. Ventonghen na Tottenham ya samu jan kati a wasan da aka gwabza a filin Wembley inda aka tashi 3-1.#
Zakarun Faransa Monaco sunyi kunnen doki da Leipzig na Germany a wassan da aka tashi 1-1 a filin Red bull Arena.
Ga dai yadda aka kaya a gasar cin kofin zakarun turai cikin rukuni na farko
Real madrid 3-0 Apoel Nicosia
Fayenoord 4-0 Manchester city
Liverpool 2-2 Sevilla
Shakhtar donetsk 2-1 scc Napoli
Maribor 1-1 Spartak moscow
Fc Porto 1-3 Besiktas
Leipzig 1-1 Monaco
Tottenham 3-1 Dortmund
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng