ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan bindiga sun kai hari gidan gonar shugaban hukumar EFCC

Majiya sun shaida wa manema labarai cewa yan bindigar sun sace shanu da tumakai.

Bisa ga rahotannin lamarin ya faru ne a daren ranar talata a gonar dake kauyen Karshi dake wajen garin babban birnin tarayya.

A kwanan baya ne shugaban EFCC ya gama gina gidan da zai zauna a cikin harabar gonar amma bai kai ga tarewa.

Wannan shine karo na biyu da yan bindiga zasu kai hari ga jamí'in hukumar EFCC. A wancan karon sun kai harin ne dai dai ofishin hukumar dake nan Wuse a garin Abuja tare da yin harbe-harbe kana suka aje wata wasika mai dauke da barazanar kashe wani jami'in hukumar mai suna Ishaku Sharu.

Karanta labari shugaban ke cewa>>Da taimakon majiya mun gano naira biliyan 29

ADVERTISEMENT

Shi dai Ibrahim Magu a halin yanzu yana fama da wadanda ake zargi da yi wa tattalin arzikin zagon kasa bisa ga rawan da yake taka wa wajen ganin an hukunta su.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT