ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon shugaban kasa ya caccaki gwamnatin buhari

Jonathan yace gwamnatin Buhari na karya ne kuma tana sako labari mara tushe

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kira gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin ƙarya da yada labari mara tushe.

Jonathan yayi wannan tsokacin yayin da ya amshi bakoncin daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban jam'iyar PDP Farfesa Tunde Adeniran tare da tawagar magoya bayan sa a garin Abuja ranar alhamis 19 ga watan octoba.

Jigon jam'iyar adawa ta PDP yace gwamnatin Muhammadu Buhari na cike da ƙarya da yaɗa jita-jita mara tushe.

Jonathan yayi iƙirari cewa gwamnatin PDP tayi kokari a shekaru 16 da take mulki wanda tunda da gwamnatin mai ci ta hau shekaru biyu baya bata tsinana ma komai ba har yanzu.

ADVERTISEMENT

Yayi korafi ga ministan wuta Babatunde Fashola inda yake cewa;

"A fannin samad da wuta mun yi iya bakin kokarin mu wajen bunkasar da ita. Amma a lokacin mulkin mu wani gwamna yace indai gwamnatin mai kishin kasa ne zata iya magance kalubalen dake tare da fannin wuta cikin watanni shidda"

"Yau dai APC ke mulki kuma wannan gwamnan shine ministan samad da wuta, yau kusan kusan shekara nawa kenan da suke mulki?" ya kara.

Daga karshe Jonathan yayi kira ga yan jam'iyar PDP da su tabbatar sun zabi shugaban jam'iya mai ƙishi da kuma mai gwanintar yin abu mai kyau kuma mai tattare da karfin hali domin jagorantar jam'iyar wajen samun nasara a zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT