ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Idan kinji haushin rashin aurena ki turo min lambar mahaifin ki - martanin da Maryam Booth ta mayar ma wata da ta nema ta da bakar maganar

Ita dai wannan ma'abociyar ta gamu da dodon ta yayin da ta kai bakan magana shafinta

Fittaciyar jarumar masana'antar Kannywood Maryam Booth ta mayar ma wata ma'abociyar shafinta da martani mai radadi bisa ga bakan maganar da tayi.

Lamarin ya faru ne sanadiyar sakon talla da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram na wata garabasa da Jaruma empire wanda ke safarar kayan ma'aurat ke bada wa ga kustomomin ta.

Sako ne ga duk mai son samun garabasa amma wata mai suna @fadeelamatawalle mai bibiyan shafinta tayi mata mummunar fassara.

"Allah ya kyauta ya shirya ki. Ashe duk irin ku daya ne. koda yake yanzu nagan Allah ya fara shiryata tanasa dan mayafi.

ADVERTISEMENT

jaruma mai naira kuma mai kyautar nairori ashe tana baki kudi?. Ashe kina amsan kaya shiyasa kika kasa aure duk da gorontulan da lakanin nata". ta rubuta.

Sakamakon abun da ta rubuta jarumar ta mayar mata da martani kamar haka; " Baki da labari?  tana bani kudi kam ba karya.

Allah sarki gaki yarinya karama sai uban Shishigility but I don’t blame u I blame tsohuwarki da bata baki tarbiyar “mind ur business ba” ur too young for all this and inkinji haushin rashin aurena DM me ur fathers number".

Suma  ma'abotan shafin Maryam ta instagram sunyi tsokaci game da maganar da ita @fadeelamatawalle tayi inda suma suka yi mata zaren mikiya da maganganu.

Karanta inda jarumar tace Tana neman tsari daga mutanen banza

ADVERTISEMENT

Yayin da ita dai wannan baiwar Allah ta gamu da uwayen gidan ta wajen yi bakar magana, wasu daga cikin masoyan Maryam Booth na ganin tayi tsanani da irin martani da mayar domin a matsayin ta na jaruma wanda ake koyi da ita bai kamata ta biye mata ba har ma ta mayar mata da bakar magana.

Hakazalika wasu na ganin bai kamata ta sanya mahaifinta a cikin martanin da ta mayar mata.

Karanta inda shima Adam Zango ke cewa zai saka wando daya da masu masa zargin karya

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT