ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

‘Buhari’ ya shiga gidan wakafi bayan ya damfari wani sanata

Dan damfarar wanda yayi shigar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya damfari dan majalisar dattawa wanda ke wakiltar jihar niger ya gamu da kiarshen shi

An gurfanar da wani amshakin ɗan damfara gaban kotun majistere wadda ya wayence da cewa shi sarkin garin Lapai ne domin ya damfari wani sanata mai wakiltar yankin kudancin jihar niger.

Ana tuhumar Muhammed buhari kamar yadda Total media bisa ga zargin damfarar sanata Mustapha SaniN400,000 bayan ya wayence da sarkin garin Lapai Alhaji Umaru Tafida.

Bisa bayanin dan sandan da ya gurfanar dashi gaban kotu Abdullahi Aliyu, sanatan ya kai kara Buhari  ga ƙwamishnan yan sanda na jihar niger.

Abdullahi ya fada ma kotu cewa;

ADVERTISEMENT

“sanata Aliyu ya samu kiran waya cikin watan Yuli da ya gabata daga wani da ya wayance da sarkin Lapai. Yace yana neman taimako kudi daga sanatan domin ya aiwatar da wasu ayuka a fadar shi.

Bayan kiran shine sanatan ya tura mai N400,000 ga banki.

Yayin da dan majalisar ya ziyarci sarkin a fadar shi cikin watan Agusta shine sarkin ya bayyana mai cewa ba shi ya kira shi ba kuma bai nemi kowa ba da taimakon kudi.

Yayin da jami’an yan sanda ke bincike aka gane cewa Buhari ya samu taimako daga Fatima Muhammed Hausa isa wajen damfarar dan majalisar”.

Jami’in ya nemi kotu da ta daga ranar jin kara domin su kammala bincike kuma ya kara da cewa laifin ya sabawa ƙundin tsarin mulkin jihar sashe na 97.

ADVERTISEMENT

Shugaban kotun Mohammed Gabi ya ba wanda ake zargi damar yin beli da N100,000 har zuwa ranar da zasu saurari hukuncin kotu.

Kotu ta daga ranar jin karar zuwa 4 ga watan Octoba na bana.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT