ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Boko haram ta saki sabon faifan bidiyo

Cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna 20, daya daga cikin yan matan da tayi magana ta sanar cewa dukkanin yan matan Chibok da aka kama sunyi aure bisa yardar jagoran kungiyar Abubakar Shekau.

Kungiyar Boko Haram ta saki sabon faifan bidiyo mai nuna yan matan Chibok tare da daukan nauyin haifar da hatarin jirgin sojojin sama.

A bidiyon da aka saki ranar litinin 15, wasu yan mata wadanda ake sa ran cewa yan mata matan chibok ne sunyi magana cewa baza su koma gida ga iyayen su idon su rufe da Nikabi.

Cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna 20, daya daga cikin yan matan da tayi magana ta sanar cewa dukkanin yan matan Chibok da aka kama sunyi aure bisa yardar jagoran kungiyar Abubakar Shekau.

ADVERTISEMENT

"Mune yan matan Chibok. Da yardar Allah baza mu koma gida gare ku. muna zama cikin walwala, babu abun da muka rasa domin yana bamu dk abun da muke nema." tace.

Duk da ikirarin da kakakin sojojin Nijeriya Birgediya janar Sani Usman yayi na cewa Shekau yana fama da matananciyar rashin lafiya. A cikin bidiyon shugaban kungiyar yayi harbin bindiga  tare da yin huduba na tsawon minti 13.

Duk a cikin bidiyon, za'a gan inda yan ta'addar ke kokari harbin jirgin saman sojojin Nijeriya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT