ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan ta'adda sun kai harin kwantar bauna jihar Adamawa

Sun kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu kana sun kona gidajen jama'a a harin da suka kai cikin dare a garin Pullam dake karamar hukumar Madagali

Bisa rahoton da Premium Times ta fitar yau 16 ga wata, mazaunin garin shaida masu cewa farmakin ya dauki tsawon lokaci kimanin sa'o'i 3 wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wani shaidar gani da ido Adamu Japhet ya zartar wa manema labarai cewa yan ta'ada sun gabatarb da harin kwantar bauna da misalin karfe 11 na dare inda suka yi ruwan alburusai tare da kona gidajen mutane kana suka yi garkuwa da wasu mutane.

Yana mai cewa " Da kyar na kubita. Na dan yi kwantar bauna ne kana na tsere zuwa wata maboya, babu sojjan da ya zo ya ceci mu. A halin yanzu dai ba zan iya kayyade adadin mutanen da suka mutu sanadiyar farmakin. Abun bakin ciki ne!".

Dan majalisar dokoki na jihar adamawa mai wakiltar karamar hukumar Madagali da Michika Adamu  Kamale ya tabbatar da harin inda ya kara da cewa yan ta'addar sun kashe dabbobi yayin da suka far ma al'ummar garin Pullam.

ADVERTISEMENT

Yace " Na samu kiran waya winda ake sanar mun cewa sun kai farmaki Pallam. A halin yanzu da nake magana, ba samu adadin mutanen da suka mutu amma sun kashe jama'a da dama kuma sunyi garkuwa da wasu tare da kona gidajen jam'a.

Kafin wannan harin, yan ta'addar sun kai farmakin yankin Wanu da Kamale da Kafin Hausa. Kusan kullum kenan suka kawo hari a yabnkin, ya kamat gwamnati ta nemi mafita"

"Muna bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ziyarci mu domin irin halin da muka shiga sanadiyar hare-haren yan ta'addar".

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT