ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An sallami wakilin gidan rediyo na Freedom fm daga jerin yan jaridar gidan gwamnatin jihar Kano

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja

Gwamnatin jihar Kano ta sallami wakilin gidan rediyon Freedom fm Abbass Yusha’u daga cikin yan jarida dake kawo rahoton gidan gwamnati.

Wannan sallamar tana da alaka da labarin da wakilin ya fitar a baya na arangamar da gwamnan jihar yayi da yan fashi da makami a hanyar sa na zuwa garin Jos daga Abuja.

A baya dai wakili daga ofishin yada labarai na gwamnatin ya tabbatar da labarin amma daga baya gwamnatin ta musanta haka.

Bayan aikawan da tayi ga gidan rediyon freedom fm na janye Abbas gwamnatin ta samu wani da zai maye gurbin sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT