ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan tsohon mataimakin shugaban ƙasa yaji ba dadi daga kotu

Kotu ta sake shi bayan an garkame shi bisa ga dalilin bijirewa umarnin kotu na kin dawowa da dansa da ya dauke daga wajen tsohuwar matar sa

Babban dan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Aminu Abubakar ya samu rangwame bayan kotu ta sake shi bayan an garkame shi bisa ga laifin kin bin umarnin kotu game da rainon yaran su 2 da ya dauke daga wajen mahaifiyar su.

Mai shari'a Kikelomo Ayeye na kotun majistere ta bada umarni na garkame shi har sai ya kawo dan su Amir mai shekaru 6 wanda ya dauke daga wajen mahaifiyar su.

Kotu ta baiwa mahaifiyar damar kula da yaran har zuwa 1 ga watan Nuwamba na bana inda za'a kara jin kara game da ainihin wanda zai dauki hakkin rainon su.

Aminu Abubakar ya rabu da matarshi Umma Fatima Bolori a 2011 wanda tun bayan rabuwar suke halin kare jini biri jini game da rainon yaran su.

ADVERTISEMENT

A ranar 11 ga watan octoba Mahaifiyar su ta samu umarni daga kotu na kula da yaran bisa ga kukan da kai na cewa yaran wadanda a lokacin suna wajen mahaifin su basu samun kulawar uwa.

A kwanan baya mun sako wata labari mai nuna inda shi Aminu tare da tsohuwar matar shi Umma Fatima suke rigima a makarantar diyar su game da raino har ma abun ya kai ga zuwa ofishin ƙwamishnan yan sandan jihar Legas.

Takardar kotu ya nuna cewa diyar su mai shekaru 8 ta tura ma mahaifiyar su sakonnin ta waya inda take fada ma uwar cewa basu jin dadin zama da mahaifin su kuma lalle wajen ta suke son zama.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT