ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Zan yi iya bakin kokari na wajen kubitar da duk dan kasa dake garkame a hannun Boko Haram

Shugaban yayi wannan alkawarin yayin da amshi bakoncin malaman jami'ar Maiduguri da yan ta'adar suka saki kwanan baya.

Shugaban yayi wannan alkawarin yayin da ya amshi bakoncin malaman jami'ar Maiduguri da yan ta'addar suka saki kwannan baya a fadar sa dake nan Villa.

Malaman suna cikin tawagar masana wajen gano danyen mai a yankin tafkin Chad dake nan jihar Borno.

Tare da malamai, shugaban ya gana da mata 10 da yan ta'addar suka yi awon gaba dasu.

Malaman da matan sun fito daga zauren yan ta'adar ranar 10 ga watan Febreru 2018 bayan yarjeniyar da ya faru tsakanin yan ta'addar da gwamnatin tarayya.

ADVERTISEMENT

"Farin cikin dake tattare dani baya iya misaltuwa ganinwadanda yan ta'adar boko haram suka sace. Zamu dauki duk wani mataki da ya kamata wajen ganin cewa mun kubitar da duk wani dan kasar dake hannun yan ta'adar. Rayuwar  ko wani dan kasa yana da muhimmanci. Shugaban ya sanar.

Ya nun farin cikin sa ganin cewa malaman da matan sun koma ga iyalin su tare da yin kira da sauran yan kasar da su taya su murna.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT