ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An kai hari ofishin yakin neman zabe na Atiku dake jihar Katsina

maharan sun kai harin ne a daidai karfe 8:00 na daren ranar asabar 7 ga wata kuma sakamakon harin sun faffasa gilasan motoci da sauran sassa na motocin dake ajiye a harabar ofishin

Harin dai ya faru yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta'aziya jihar ga iyalen tsohon dan majalisar dattawa Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu kwanan baya.

A bisa labarin da jaridar Premium times tayi, maharan sun kai harin ne a daidai karfe 8:00 na daren ranar asabar 7 ga wata kuma sakamakon harin sun faffasa gilasan motoci da sauran sassa na motocin dake ajiye a harabar ofishin.

Kamar yadda mai kula da ofishin mai suna Masa'udu Abdulkadir ya sanar,  babu wanda ya jikkata sakamakon harin da aka kai. Yace ana gyara ne a harabar sanda maharan suka kai harin.

Ya kuma kara da cewa, wannan lamarin ba zai hana yan goyon bayan Atiku cigaba da nuna goyon bayan su bisa kudirin sa na karawa da shugaba Buhari a zaben kasa da zai gudana a shekara mai zuwa.

ADVERTISEMENT

A wata sanrwa da ya fitar, kakakin rundunar yan sanda na jihar Gambo Isah ya sanar cewa hukumar ta kama wasu da ake zargin suna cikin wadanda suka kai harin su uku kuma nan bada dadewa ba za; a gurfanar dasu gaban kotu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT