ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Uwargidan shugaban ƙasa ta ƙaddamar da shirin koyama mata 1,000 sana’a a jihar Kwara

Uwargidan tace wannan yana daga cikin tsare-tsare na gwamnatin domin tallafa ma matasa da mata don moriyar rayuwa

Uwargidan shugaban ƙasa Aisha buhari ta kaddamar da shirin koyar ma mata 1,000 sana’ar hannu a jihar Kwara.

Aisha Buhari tace wannan yana daga cikin tsarin gidauniyar tafuture Assured programme wanda ke tallafa ma matasa da mata domin kawar da talauci a al’umma.

Uwargidan tace wannan yana daga cikin tsare-tsare na gwamnatin domin tallafa ma  matasa da mata don moriyar rayuwa.

Matar shuagaban ƙasa tayi kira ga wadanda zasu amfana da shirin da su mayar da hankali wajen koya domin a karshen shirin za’a gudanar da jarabawa.

ADVERTISEMENT

Cikin sana’o’i da za’a koya masu akwai dinki da koyar girki da ilimin na’urar kamfuta tare da aikin wuta.

Aisha Buhari tace wadanda suka ci jarabawa zasu samu kayan aiki a fannin da suka koya.

Gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed wanda kwamishnan labarai Alhaji Mahmud Ajegbei ya wakilce shi a wajen taron yace gwamnatin jihar zata iya bakin kokarin ta wajen ganin matasa da mata mata sun samu aikin yi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT