ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna yace sun samu basusuka tare da tarin bashin albashin ma'aikata yayin da suka hau kujerar mulki

Yari yace gwamnoni sun samu tarin basusuka yayin da suka shigo fagen mulkin jihohin su

Shugaban majalisar gwamnoni Abdulaziz Yari ya ƙare gwamnoni inda yake cewa wasu daga cikin su sun samu tarin basusuka yayin da suka hau kujerar mullkin jihohin su.

yayi wannan sanarwan ranar talata yayin da yake kare yan uwan shi bayan shugaban ƙasa Muhamadu Buhari ya ƙalubalanci rashin biyan albashin ga ma'aikatan jihohi.

Shugaba Buhari ya nuna bakin ciki ganin cewa duk da tallafin da gwamnatin tarayya ke baiwa jihohi suna har yanzu ma'aikatan jihohi basu samu albashin su a wasu jihohi.

Yayin da yake mayar masa da martani Gwamna Abdulaziz Yari yayi iƙirari cewa hakika tallafin da suka samu daga gwamnatin tarayya anyi amfani da ita yadda ya kamata har ma ya kara da cewa wasu daga cikin su sun samu tarin basusuka yayin da suka hau kujerar mulki.

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnoni sunyi gadon basusuka lokacin da suka shiga ofishin su cikin har da bashin tarin albashin ma'aikata.

cikin tawagar majalisar gwamnoni da suka ziyarci shugaban ƙasa akwai na jihar Ondo, Bauchi, Akwa ibom, Jigawa, Kwara da mataimakin gwamnan jihar Ebonyi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT