Rundunar sojoji na 1 Division tare da hadin gwiwar jami’an hukumar DSS sun kama yan safarar harsasai 2 a babban titin Gusau zuwa Funtua ranar lahadi 24 ga watan Satumba.
Rundunar sojoji sun kama masu safarar harsasai a babban titin Gusau zuwa Funtua
Brig.gen Sani Usman yace bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin suna hanyar su wajen isar da harsashen wajen yan fashi
A wata takarda da aka fitar ranar litinin kakakin rundunar sojoji na kasa Brig.gen Sani Usman yace bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin suna hanyar su wajen isar da harsashen wajen yan fashi.
Usman yace an kama su cikin motar "Golf Volkswagen" mai dauke da lamba AWE-534-AA na jihar Nasarawa tare da kunshin harsasai 1,479.
Bisa ga bayanin shi, a yanzu wadanda ake zargi suna hannun hukumar DSS.
Kakakin ya sanar cewa rundunar sojoji da aka aika garin Dangulbi dake karamar hukumar Maru na jihar Zamfara sun kama wasu yan fashi kwannan baya yayin da suke safarar tabbatar da tsaro.
Ya kara da cewa rundunar sun kama wani barawon shanu mai suna Abdullahi Jummo Nakogiwo a garin Dalingen dake karamar hukumar Rabah na jihar Sokoto.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng