ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wani direkta ya kashe kansa sanadiyar reshin biyan albashin wata 11

An samu gawar shi na yawo saman bishiya a kasuwar mammy dake nan barikin sojoji na Maigumeri

Wani mai ruwa da tsaki na ma'aikatar farar hula na jihar Kogi mai suna Edward Soje ya kashe kansa ta hanyar rataya a garin Lokoja babban birnin Jihar Kogi.

Bisa ga labarin da NAN ta fitar An samu gawar shi na yawo saman bishiya a kasuwar mammy dake nan barikin sojoji na Maigumeri.

Ma'aikacin mai shekaru 54 ya kashe kansa bayan kwana 10 da samun karuwar jerin yara uku wanda matar sa na shekara 17 ta aifar masa wanda tunda suka yi aure basu samu yara ba.

Soje wanda dan asalin garin Ogori na karamar hukumar Ogori-Magongo bai samu albashin sa na wata 11.

ADVERTISEMENT

Kafin rasuwar sa yayi yadda zango zuwa garin Abuja inda matar sa take wanda daga bisani ya ajiye mata da wasika na bankwana.

cikin wasikar soje yayi ma matar sa tare da jariran ta fatan alheri da samun nasara a duniya kuma yayi masu adua.

Majiya daga iyalin shi sun shaida ma manema labarai cewa Soje tun kafin rasuwar sa ya shiga tsaka mai wuya sanadiyar rashin biyan albashin sa na wata 11.

Yana daya daga cikin ma'aikatan dake bin gwamnatin jihar Kogi albashin watannin da dama.

Bukatun yau-da kulum ya sa ya siyar da motar sa da gidan sa da yake ginawa a garin Lokoja.

ADVERTISEMENT

A bisa labarin majiya, kuncin Soje ya karu yayin da matar sa ta haifi yara uku a wata asibiti mai zaman kansa dake Abuja.

sauran kwana daya da yin bikin sunan yaran Soje ya koma Lokoja domin daukan sauran kudi da ya rage a asusun bankin sa.

ya koma Abuja inda ya mika ma matar kudin wanda wa she gari aka gudanar da bikin suna a asirce bayan yayi ma matar karya cewa zai dauko wani abu daga gida ya dawo amma dawowar ke da wuya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT