ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sojoji sunyi arangama da wadanda suka kai hari al'ummar Ancha

mutane 5 sun rasu yayin da wasu da dama suka ji rauni

Rundunar sojoji sun kashe wasu mutane 5 da ake zargi cewa suna daga cikin wadanda suka kai hari ga al’ummar Ancha dake karamar hukumar Bassa na jihar Filato.

Bisa ga rahoto da premium times ta fitar ranar litinin 11 ga watan Satumba,jami’an tsaron sun bayyanar cewa sun kashe wasu da suke zargi da kai hari ga al’ummar Ancha.

A wani rahoto tawagar rundunar sojoji ta musamman sunce sun kashe wasu mutane 5 da suke zargin cewa sune suka kai harin ga al’ummar Ancha wanda yayi sanadiyar rasa rayuka 19.

Kakakin tawagar captain Adamu Umar yace “ banda mutane 5 da muka kashe akwai wasu da dama da suka ji rauni.”

ADVERTISEMENT

Captain Umar ya ce wani daga cikin rundunar sojoji ya rasu yayin da wani yaji rauni sanadiyar arangamar da suka yi.

Captain Umar ya bayyanar cewa rundunar sojoji sun mamaye kauyen Ancha don neman sauran mutanen da suka gudu.

Shi dai Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna bacin ran sa game da harin da yayi sandiyar kashe rayka 19 kuma ya umurce jami’an tsaro da su kama wadanda suka aikata laifin.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT