ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An rantsar da sabon sanata mai wakiltar jihar Taraba maso arewa

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya rantsar da sabon sanatan wanda ke karkashin jam’iyar PDP

Nigerian Senate

An rantsar da Shuaibu Lau ranar 5 ga watan Yuli a matsayin sanata mai wakiltar jihar taraba maso arewa.

Shuaibu zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan jihar Taraba Sani  Abubakar Danladi, wanda kotun koli ta kora ranar 23 ga watan Yuni.

Shuaibu ya kai karar hukunci da kotun daukaka kara ta dauka inda yake inkari cewa shi ya ci nasarar zaben amma kotun ta sauya hakkin shi.

Kotun koli ta bashi nasarar kuma ta umurci Danladi da ya nade tabarman shi tunda mai wuri yazo kuma ya mayar da duk wani albashi da alawus da ya amsa cikin kwana 90.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT