Kotun koli ta ƙaddamar da Ahmed Makarfi a matsayin ainihin shugaban jam’iyar PDP na kasa.
Kotun koli ta kori Sheriff ta nada Makarfi a matsayin ainihin shugaban jam’iyar PDP
Kotun koli ta kori Sheriff wanda a baya kotun ɗaukaka kara dake jihar Rivers ta tabbatar cewa shine sahihin shugaban jam’iyar.
A zaman da kotun tayi ranar laraba 12 ga watan Yuli, kotun ta yanke huƙunci na kori Ali Modu Sheriff wanda a baya kotun ɗaukaka kara dake jihar Rivers ta sanar cewa shine sahihin shugaban jam’iyar
Wasu ‘yan goyon bayan Makarfi suka kai karar kotun koli inda ma suka cimma burinsu don ganin shine sahihin shugaban jam’iyar.
Tun ba yau ba Makarfi da Sheriff ke gumurzu a kan shugabancin jam’iyar.
Riƙicin shugabancin jam’iyar ya karfafa lokacin da aka cire Sheriff a matsayin shugaba a taron jam’iya da aka gabatar a ranar 21 na watan Mayu na shekarar bara inda jam’iyar ta kafa kwamitin rikon kwarya wanda aka sa Makarfi a matsayin jagora.
Yan jam’iyar da dama sun goyi bayan Makarfi na zama shugaban jam’iyar cikin su akwai wasu tsofofin gwamnoni da yan majalisa.
Wannan riƙicin ya sa wasu yan jam’iyar da dama sun bar jam’iyar zuwa jam’iyar adawa APC har ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya yi alkawarin barin jam’iyar idan kotun koli bata tabbatar da makarfi a matsayin jagoran jam’iyar
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng