Wata ƙungiyar matasa mai suna ‘matasan nijeriya masu neman adalci’ watau “Nigerian Youth Advocate for Justice” sun ƙalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da yayi murabus kasancewar barin kasar da ya yi har kwana 53.
Ƙungiyar matasa sun ƙalubalanci shugaban kasa da ya yi murabus cikin maƙonni 8
ƙungiyar tace matasa miliyan bakwai zasu tsige shi daga mukamin shi idan bai yi murabus
Ƙungiyar ta ba shugaba makonni 8 da ya yi murabus ko kuma matasa miliyan 7 daga jihohi 22 zasu tsige daga mukammin shi.
Shugaban ƙungiyar, Seriki Olorunwa yace, rashin lafiyar shugaban kasa yasa ba zai iya cigaba da mulkin kasar.
“Muna kira ga majalisar dattawa, majalisar wakilai, majalisun jihohi da sauran su da su yunkura wajen ganin cewa shugaba ya yi murabus don amfanin yan kasa.’ Olorunwa yace.
Ya kara da cewa matasa a shirye suke wajen cimma buri su har ma ya bada tabbaci cewa wannan zai faru ba tare da zubar da jini.
Dangane ga kashe-kashe, garkuwa da mutum da kuma sace-sace dake yaduwa a kasar, ƙungiyar tace jam’iyar APC ta wulakanta yan nijeriya don son kai.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng