ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mutum 19 sun rasa ran su kuma 23 sun ji rauni sanadiyar harin da yan ta’adda suka kai

Harin wanda aka gudanar yammacin ranar talata yayi sanadiyar rasuwar mutum 12 ciki akwai jami’an tsaro (CJTF) guda 12 da wasu yan farin kaya 6.

A Nigerian soldier patrols on the outskirts of Damasak in northeastern Nigeria as peace returns after years of trouble from Boko Haram insurgents

Jami’in yan sanda na jihar Borno sun tabbatar a ranar laraba cewa mutum 19 suka rasa ran su sanadiyar harin da yan ƙungiyar boko haram suka kai a yammacin ranar talata a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

ƙwamishnan yan sanda na jihar Borno mista Damian Chukwu ya bayyana cewa an gudanar da harin a yammacin ranar talat wanda yayi sanadiyar rasuwar wasu jami’an tsaro na CJTF guda 12 da yan farin kaya 6.

Kamfanin dillacin labarai (NAN) suka kawo rahoto mai nuna cewa akalla mutum 860 na jami’in tsaro na CJTF suka rasa rayuka sanadiyar hare-haren da ƙungiyar ‘yan ta’adda ke yi a jihar tun shekarar 2014.

Chukwu ya zayyana ma manema labarai cewa mutum 23 sun ji rauni sanadiyar harin

ADVERTISEMENT

ƙwamishnan wanda ya ziyarci guraren da aka gudanar da hare-haren ya ce, wasu yan mata hudu masu kunar bakin wake suka kai harin a shiyyar Moloi, Judumeri da Polo-Sabongari  dake Maiduguri.

Wannan yana cikin hare-hare da ƙungiyar boko haram ta gudanar tunda ta fara yakin ta’addanci a shekara 2009.

Sun kai hari a wurare da dama cikin su akwai jami’ar maiduguri wanda suka kashe mutum hudu, offishin majalisar dinkin duniya (UN) dake Abuja, babban offishin yan sanda na Abuja tare da harin da suka kai garin Nyanya wanda ya kashe mutane da dama.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT