ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Madalla! Uwargidan shugaban kasa ta iso London don ganin Shugaba Buhari

Mataimakin uwargidan ta sanar da haka a shafin ta na twitter.

First Lady, Aisha Buhari returning from London on June 6 after meeting with President Muhammadu Buhari

Hakika uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta iso garin London yau ranar 5 ga watan Yuli don ganin mijinta Muhammadu Buhari a inda yake jinyar rashin lafiya

Uwargidan ta bar Nijeriya ranar asabar 1 ga watan Yuli inda ta fara tsayawa a kasar habasha don halartan taron matan shugabannin kasashen afrika wanda aka yi ranar litinin 3 ga watan Yuli.

Mataimakin ta Zaynab Ikaz-kassim ta sanar da isowarta birnin London a shafin ta na twitter.

Ta rubuto, “ mai girma Aisha Buhari ta iso birnin London a safiyar yau bayan sa’o’i 7 cikin jirgi daga kasar habasha, inda ta halarci taron bikin shekara 15 na matan shugabannin kasashen afrika”

ADVERTISEMENT

In zamu tuna, bayan dawowarta daga tafiyar farko na ganin  mijinta ranar 6 ga watan Yuni Aisha Buhari tace “ mijina na samun sauki, kuma nan ba da jimawa zai dawo kasar don cigaba da alamuran shugabanci.”

“Ina ma yan Nijeriya godiya da adduo’in da kuke yi wa mijina. Shugaba yana gab da dawowa”.

Shugaba Buhari ya bar kasar 7 ga watan Mayu don  neman saukin rashin lafiya da yake fama da shi, inda ya ba mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo tutar shugabanci

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT