A zaman kotu da aka yi ranar laraba 16 ga wata, alkali Daniel Longji ya ki amincewa da bukatar belin da tsohon gwamnan ya nema a daga ranar zantar da hukunci har sai bayan ya gama nazari kan karar shi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da karar inda take zargin tsohon gwamnan da yin sama da fadi da makuden kudin jihar har Nera biliyan shida da miliyan dubu uku.

Hukumar EFCC tana tuhumar Jonah Jang da wawure Nera 6.3bn daga cikin zargin laifuka 12 da take yi masa da suka hada da almubazaranci da karkata kudin jama'a, cin amana da rashin gaskiya amma ya musanta dukansu.