Wasu yan fashi da makami sun kai hari gidan shahararren marubucin hausa na masanaantar Kannywood wato Yakubu M Kumo.

Kamar yadda abokin sana'ar shi Ibrahim Birniwa ya bayyana a shafin sa na Instagram Kumo ya dan samu rauni wajen gwagwarmaya da yayi dasu wajen tokare kofar falonsa don hana su shiga.

Abun godiya game da fashin shine ganin cewa barayin basu ji  masa mummunar rauni wanda har sai an kwantar dashi a asibiti.