Cikin Mutane shidd da shugaban ya nada har da barister Festus Keyamo wanda aka nada kwanan baya a matsayin kakakin yakin neman zaben zarcewan shugaban a zaben 2019.

Wannan labarin ya fito ne  a wata wasika da shugaban ya tura ga yan majalisa domin yardar su, wanda shugaban majalisar Bukola Saraki ya karanta a zaman da suka yi ranar talata 8 ga watan Mayu.

Ga sunayen sauran mutanen da ya nada kamar haka: Chief Olabode Akeem Mustapha daga jihar Ogun, Alhaji Garba Buba daga jihar Bauchi, Bello Garba (jihar Sokoto) Brigadier-General Joseph O.J Okalogu (jihar Enugu), Mustapha Adewale Mudashiru jihar Kwara), Mr Adewale W. Adeleke (jihar Ondo).

Bayan ga haka, shugaban ya tura sunan Ateru Garba Madami, a matsayin wanda zai maye gurbin kwamishnan hukumar zabe na jihar Niger.