Mahaifin shahararren mawakin gambara na arewa King Bawa wanda aka fi sani da Kheengz ya rasu.

Mawakin wanda ya shahara a fannin wakar hip-hop ya sanar da labarin rasuwar ne a shafin sa na dandalin sada zumunta.

Kamar yadda ya sanar mahaifin sa ya rasu ne ranar alhamis 13 ga watan Satumba.

Yana mai mika sakon godiyan sa ga dinbim masoya da suka taya shi jaje tare da yin kira ga sauran jama'a da su taimaka su cigaba da yi masa addua'a.