Za'ayi jana'izar shi ranar laraba da zaran gawar shi ta dawo Nijeriya.

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a 'yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya.

Marigayin, fitaccen malamin addini ne kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya kafa kamafanin Isyaka Rabiu and Sons.

Ya rasu ya bar mata da yara da jikoki da yawa. Cikin yaran sa akwai Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, shugaban kamfanin BUA da Nafiu Isyaka Rabiu shugaban kamfanin jirgin sama ta IRS.

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Qur'an".

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.