Mai tsaron bayan mai suna Hussaini Isah ya rasu a yammacin ranar litinin 14 ga watan mayu, sakamakon hatsarin babur da samu a dai dai kofar gidansu dake yankin Maitunbi nan garin Minna.

Kungiyar ta sanar da labarin mutuwar sa a shafin ta na Twitter tare da taya iyalensa da masoyan kungiyar ta'aziyar babban rashi da aka samu.

Hazikin dan kwallon wanda aka fi sani da Babayaro yana daga cikin yan wasan kungiyar da suka kaya da tawagar Kwara united ranar lahadi 13 ga wata a wasan wanda aka tashi da kunnen doki (1-1), a gasar firimiya ta Nijeriya.

kamar yadda rahotanni suka bayyana, an tabbatar da rasuwar sa yayin da ake kokarin garzaya dashi asibiti bayan da babur ta buge shi.

Hussaini Isah tare da amaryar sa

Sai dai dan wasan ya rasu ya bar iyayen sa da amryar sa wanda aka daura auren su wata biyu baya.

Wannan shine karo na biyu da dan wasan wata tawagar kungiyar wasan kwalo kafa ta Nijeriya zai rasu.

a cikin watan Febreru na bana, mai tsaron bayan kungiyar Kano Pillars ya rasu sakamakon hatsarin mota da yayi hanyar shi na zuwa gida bayan wasan su da Enyimba.