Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon shugaban hukumar yan sandan farar kaya.

Kakakin shugaban Garba Shehu ya sanra da labarin haka ranar alhamis 13 ga watan Satumba

Kakakin ya kara da cewa sabon shugaban hukumar cikakken jami'in hukumar ne ciki-da-waje kuma ya samu horo mai tarin yawa.

Yusuf Magaji Bichi zai maye gurbin  Mathew Seiyefawanda aka nada a matsayin shugaban hukumar mai rikon kwarya a ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nada shi bayan da ya sallami tsohon shugaban hukumar Lawal Daura.

Sallamar shi ya biyo bayan mamayar da jami'an hukumar suka yi ma zauren majalisar tarayya inda suka hana ma'aikata da yan majalisar shiga ko fita.