Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, bai boye farin cikin sa bisa zanen da wani fasihin yaro mai shekaru 11 yayi masa yayin da halarci taro a jihar Legas.

A taron wanda aka shirya musamman domin raya al'adar kasar Afrika, yaron mai suna Kazeem Olamikan ya zane hoton shugaban cikin sa'o'i biyu.

[No available link text]

Bikin taron wanda aka gudanar a dandalin shakatawa ta "Afrikan Shrine" ya samu halarcin manyan fuskoki na daga cikin yan siyasa da masu ruwa da tsaki a dandalin nishadantarwa da fitattun mawaka.

A wata sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter, shugaban ya bayyana cewa yaron ya birge shi kuma ya jinjina ma basirar da Allah ya bashi.

[No available link text]

Ziyarar shugaban kasar Faransa zuwa Nijeriya

Bayan tattaunawar da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kasar Faransa ya yada zango jihar Legas domin ziyartar shingen "african shrine".

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, shugaban  shine na farko da zai kai ziyara dandalin "Shrine".

Shugaba Emmanuel Macron, ya shaida cewa a cikin shekarar 2004 yayi aiki a ofishin jakadanci  dake nan Legas kuma a lokacin ya kan ziyarci dandalin domin tunawa da al'adar Afrika.

A jawabin sa yayin da yake ganawa da manema labarai, matashin shugaban ya bayyana cewa dalilin da yasa zai kai ziyara wurin shakatawar shine domin wuri ne na raya al'adar Afrika.