Pulse.ng logo
Go

ZIyara Shugaba Buhari ya iso jihar Enugu inda zai yadda zango kana ya ziyarci Ebonyi da Anambra

Shugaban ya fara ziyarar kwana biyu da zai yi a jihohin kudancin Nijeriya

  • Published:
Shugaba Muhammadu Buhari play

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka jihar Enugu inda zai yada zango kana ya cigaba da ziyarar kwana biyu zuwa jihohin Anambra da Ebonyi cikin kwana biyu.

Kakakin shugaban ta kafar watsa labarai ta intanet Bashir Ahmad ya sanar cewa gwamnan jihar Enugu  Ifeanyi Ugwuanyi da na Abia Okezie Ikpeazu  da Okezie Ikpeazui na Ebonyi da wasu sarakuna yankin suka tarbi shugaban a filin jirgin jihar Enugu.

Bayan ziyarar da ya kai ma shugaban a fadar sa dake Villa, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace ziyarar da shugaban zai kai ga yankin zai taimaka wajen bunkasa kyakyawar halaka tsakanin al'ummar yankin da gwamnatin tarayya wanda shugabancin jam'iyar APC ke jagoranta.

Dangane da ziyarar da shugaban zai kai ga yankin, ƙungiyar mai faffitikar kafa kasar Biyafara ta IPOB ta fitar da wani takarda ta hanyar kakakin ƙungiyar Emma Powerful ranar litinin 13 ga wata inda suke yiwa shugaban gargadi na ya tsoke ziyarar da zai kai yankin.

Kakakin yace zuwan shugaban ga ƙasar Biyafara zai haifar da rikici a yankin kuma zai sanya mutuncin gwamnonin da sarakuna da suka karbi bakoncin shugaban ya zube a iduwan yan ƙungiyar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement