Pulse.ng logo
Go

Adams Jagaba "Buhari ba Allah bane kuma ba annabi ba, idan bai daidai ba zamu take shi" Inji dan majalisar wakilai

Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.

  • Published:
Jagaba Adams Jagaba play

Jagaba Adams Jagaba

(sahara reporters)

Wani dan majalisar wakilai ya soki shugaba Buhari kan sharudan da majalisar dokoki suka bashi, yace zasu tsige shi idan bai aiwatar dasu ba.

A zaman da gammayar yan majalisun tarayya suka yi ranar Laraba, sun baiwa shugaba matakai 12 wanda idan bai aiwatar ba zasu dauki mataki a kanshi kamar yadda doka ya tanada.

Hirar shi da wakilin BBCHausa, dan majalisa, Adams Jagaba mai wakiltar yankin Kachia da Kagarko na jihar Kaduna ya bayyana cewa cewa babu abun da ake fama da shi a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da ya wuce yunwa da bakar wahala.

Ya bayyana bacin ransa bisa halin ko in kula da shugaban ke nuna ga wasu matsaloli duk da cewa bincike ya tabbatar da hakan.

From left: Senate President Bukola Saraki (M), welcoming President Muhammadu Buhari to the National Assembly for the presentation of 2018 Appropriation Bill to the joint Session of the national Assembly in Abuja on Monday (7/11/17). With them is the Speaker of the House of Representatives, Yakubu Dogara. play

From left: Senate President Bukola Saraki (M), welcoming President Muhammadu Buhari to the National Assembly for the presentation of 2018 Appropriation Bill to the joint Session of the national Assembly in Abuja on Monday (7/11/17). With them is the Speaker of the House of Representatives, Yakubu Dogara.

(NAN)

 

Ya kara da cewa ba sa shakkar yiwuwar hakan don "Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi".

Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.

Sai dai zauwa yanzu, shugaban ko fadar sa basu mayar da martani kan kudurorin da majalisar take bukata daga jagoran kasar Nijeriya.

Kudurori 12 da majalisar suka shigar ma shugaba

Ga kudurorin da yan majalisar suka shigar kamar haka;

*Kawo karshen kashe-kashe a Najeriya

*A daina tsangwama da kuma muzguna wa wadansu 'yan majalisa

*Gwamnati ta rika bin doka da oda

*Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai

*Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah

*Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka shafi majalisar

*Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya don ceto demokradiyyar Najeriya

*Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya don ceto demokradiyyar kasar

*Shugaban kasa ya magance matsalar rashin aikin yi da kuma talauci a kasar

*Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara

*Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na 'yan sanda Najeriya Ibrahim Idris

*Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu.

Wannan zaman ya gudana ne a dai daia lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shugabannin majalisar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.