Pulse.ng logo
Go

Shugaban kasa Zamu sasanta da boko haram domin kubutar da yan matan da aka sace

Shugaban ya sanar da hakan ne yayin da sakataren ayyukan waje na kasar Amurka  Mista Rex Tillerson ya ziyarce shi a fadar sa dake Abuja

  • Published:
Shugaba  Buhari tare da sakataren ayyukan waje na Amurka mista Rex Tillerson play

Shugaba  Buhari tare da sakataren ayyukan waje na Amurka mista Rex Tillerson

(Boyo omoboriowo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatin sa ta dauki matakin sasanta da mayakan boko haram domin kubutar da matan Dapchi da Chibok.

Shugaban ya sanar da hakan ne yayin da sakataren ayyukan waje na kasar Amurka  Mista Rex Tillerson ya ziyarce shi a fadar sa dake Abuja.

A labarin da ya kakakin shugaban Femi Adeshina ya fitar bayan ganawar shugaban da mista Tillerson, ta ce shugaban ya shaida ma sakataren cewa gwamnatin sa na aiki da wasu masu shiga tsakani da wasu kungiyoyi kasashen waje domin kubutar da yan matan cikin lafiya ba tare da wani abu ya same su.

Shima sakataren ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka na iyta bakin kokarinta wajen bayar da gudummawar don ganin an ceto yan matan da mayakan boko haram sukla sace.

Ziyara da ya kai ma shugaban ranar litinin 12 ga watan maris, sakataren ayyukan waje da shugaba Buhari sun tattauna kan batutuwa da suka hada da yaki da ta'adanci da ayyukan jinkai a yankin ganbashin arewa da kuma tattalin arzikin kasa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement