An samu labari mai dadi daga iyalen shugaba Muhammadu Buhari inda babban diyar shugaban ta samu karuwar da namiji.

Zahra Buhari ta haihu a kasar Spain kamar yadda Lindaikeji ta ruwaito.

Labarin haka ya tabbata ta hanyar sako da hadimin shugaban kasa, Buhari sallau, ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta.

[No available link text]

Hadimin ya wallafa hotunan diyar shugaban tare mijinta Ahmed Indimi kana ya saka hoton alamar jariri a bangaren tsokaci na shafin nasa.

Cikaken bayani zai biyo nan gaba.