Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya mayar ma abokin takarar sa Atiku Abubakar martani game da batun janye takarar sa domin shi Atiku ya girmeshi kuma dan uwanshi ne wanda suke da raayi iri guda a harkar siyasa.

Atiku da tsohon gwamnan jihar Jigawa suna cikin ya'yan jam'iyar PDP dake neman zama gwanin jam'iyar da zai jagoranci ta a zaben 2019.

Yayin da ya kai ziyara jihar Jigawa ranar litinnin 10 ga watan Satumba, tsohon mataimakin shugaban kasan ya shaida ma magoya bayan jam'iyar PDP a jihar cewa zai bukaci Sule Lamido ya janye takarar sa domin shi domin su yan'uwa ne.

Ya bada hujjar fadin haka bisa ga kisan tsohon shugaban kasa da dan uwan sa yayin da suka nemi fitowa takara a karkashin jam'iyar Social democratic Party shekarun baya.

A labarin da ya bada, Shehu Musa Yar'adua ya fito takarar kujerar shugaban kasa yayin da kanin sa Umaru Musa Yar'adua ya fito takarar gwamnan jihar Katsina. Sai dai daga baya kanin ya dakatar takarar sa domin baiwa yayan shi damar cigaba da manufar don samun nasara a zaben.

A cewar shi kwatankwacin haka zai faru domin Sule Lamido kanin sa ne.

Martanin Sule Lamido

Sai dai Lamido ya mayar masa da martani inda yace hakika shi Atiku ya girme shi a shekaru amma banda siyasa kana har akwai wanda ya kamata ya janye takarar sa toh lalle Atiku ne ya kamata ya janye ma Buhari domin ya girme dukanin su.

A cikin wata takarda sanarwa da hadimin tsohon gwamnan Adamu Usman ya fitar, Lamido yace yana gaba da Atiku a harkar siyasa domin tun a cikin shekarar 1979 yake majalisar tarayya yayin da shi Atiku yake aiki a matsayin ma'akaci a hukumar Kwastam.

Lamido yace yayi hakuri kuma ya cigaba da kare martabar jam'iya duk da zagon kasa da ya fuskanta a harkar siyasa.

A cewar hadimin sa idan har akwai wanda ya kamata yan takarar PDP su janye ma takarar su toh Lamido ne domin yana da kwarewa kuma shine daidai wanda zai iya fafata da dan takarar APC.

Ya kuma jaddada cewa babu ja da baya Lamido zai yi takarar shugaban kasa idan Allah ya kai mu zaben 2019.

Lamido zai fafata da sauran jiga-jigan jam'iyar PDP dake neman kujerar shugaban kasa a zaben fidda da gwani da jam'iyar zata yi cikin watan Oktoba.