Shahararren dan majalisar wakilan tarayya, Honarabu Gudaji Kazaure, ya lashe zaben tsayawa takara karkashin jamiyar APC.

Honarabul Gudaji ya samu kuri'u  693 a zaben da aka gudanar na zama gwanin APC.

Zai sake neman wakiltar yankin KAZAURE/GWIWA/RONI/YANKWASHI a majalisar tarayya a zaben 2019.

Ga yawan kuri'u da saura abokan takarar sa suka samu kamar haka;  Muhammed Alhassan ya samu 372, Kabiru Ahmad Roni ya samu  84, Abdullahi mainasara  wanda ya samu 45, sai Nura Ibrahim  wanda ya samu kuri'u 18.