Shugaban yace za'a gudanar da zaben gwamnoni a ranar 2 ga watan Maris 2019 a sauran jihohin kasa banda jihar Anambra, Bayelsa, Kogi, Edo, Ondo, Ekiti da Osun.

*Ya dace shugaba Buhari ya zarce da shugabanci - inji Garba Shehu

Bisa bayanin jagoran hukumar za'a gudanar da zaben shugaban kasa da ta yan majalisar tarayya rana guda. Haka kuma, zaben yan majalisar jiha zata wakana rana guda da ta zaben gwamnoni a 2 ga watan maris na 2019.

Hukumar dai ta fitar da ranakun fara yakin neman zaben ga masu takara.

[No available link text]

Jam'iyu da masu takarar shugaban kasa da majalisar tarayya zasu fara yakin neman zaben tun daga ranar 18 ga watan Nuwamba na 2018 har zuwa ranar 14 na watan Febreru na 2019.

*Ya zama dole inyi iya bakin kokari na wajen mayar da taskar mulkin kasa zuwa jam'iyar PDP a zaben 2019 - Inji  Jonathan

Hakazalika yan takarar gwamna da majalisar jihohi zasu fara yakin neman kuri'u daga ranar 1 ga watan Disemba zuwa na 2018 zuwa ranar 28 na watan febreru 2019.

[No available link text]

Jam'iyu zasu fara amsar takardar takara daga babban ofishin hukumar dake Abuja tun daga ranar 17 na watan Agusta har zuwa ranar 28 na watan Agusta na 2018.

Hukumar dai ta ba jam'iyu damar yin zaben fitar da yan takarar jam'iya tare da magance duk wani matsala da ya taso sanadiyar takarar tsakanin ranar 18 na watan Agusta, 2018 zuwa ranar 7na Oktoba, 2018.