Yusuf yaji rauni sanadiyar hatsarin babur da yayi a garin Gwarinpa a daren ranar 26 ga watan Disamba na 2017.
An shirya komawa da dan shugaban kasa kasar waje domin jinya
Yusuf Buhari zai koma kasar Jamus domin samun kulawa na tsawon makonni da dama
kwana daya bayan hatsarin an yunkura wajen tafiya da shi kasar waje domin samun kulawa kan karaya da ya samu, kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
Shirin komawa kasar waje
A ranar 28 na Disamaba 2017, jaridar The Cable ta ruwaito cewa an ketara da Yusuf cikin gaggawa zuwa kasa waje.
Amma fadar shugaban kasa ta musanta wannan labari
Yusuf ya samu karaya a kan shi da kuma hanayen shi sakamakon hatsarin kana aka kwantar dashi a asibitin Cedacrest dake nan Abuja inda yake ta samun kulawa har ga zuwa yanzu.
Labari ya nuna cewa kwararrun likitoci suke kula da Yusuf a asibiti inda yake jinya.
Tafiya kasar Jamus
A rahoton da Sahara Reporters ta fitar za'a koma da Yusuf asibitin St. Josef dake yankin Wiesbaden na kasar Jamus inda zai samu kulaa na tsawon makonin da dama.
A cikin tawagar da zasu raka shi kasar akwai mahaifiyar shi Aisha Buhari da yar uwar shi Halima Buhari-Sheriff da babban liktan uwargidan kasa Dakta Kamal Mohammed tare da wasu mukarrabe uku.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng