ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sabon jeri na wasan drama a kan táshan ZeeWorld

"Young dreams" labari ne na soƴƴaya, ƙauna, abokantaka na abada, da kuma sabon farawa na rayuwa.

Sabon jeri na wasan drama a kan táshan ZeeWorld

Tashan ZeeWorld suna shiri na sakin sabon wasa mai sa zuciya dumi da tausayi. Sunan wannan jeri shi ne "Young Dreams".

Wannan labari mai nishaɗi na Indiya, ya shafi ʼ yan uwa biyu waddanda ba su taɓa yin zama tare da juna. Wasan Young Dreams ya shafi rayuwar wata yarinya mai suna Gunjan, ʼyar shekara goma-sha-bakwai. Yarinya ce mai fáraʼa da mutane, tare da ʼyar uwanta mai suna Rachna.

Balaʼi ya sami iyalinsu bayán ciwon dajì ya halaka Sneha-Mahaifan Gunjan. Bayan haka, sai Gunja taʼ koma da zama wajen ʼyar uwanta Rachna. Gunjan da Rachna suna ƙokari su daidata da zama tare, domin raʼayinsu ba iri ɗaya ba. Gunjan ta sâba da zaman ʼyanci, sai dangataka da zumunci ya yi mata wuya.

Wannan wasa na "Young Dreams"(waton Mafarki mai toho") ya shâfi neman bayani akan samartaka. Waddanan ʼ yan mata, sun shiga tuƙa shaʼanin samartaka tare, da kuma taimakon juna duk da sharadaɗin matsalolin da suka samu. Daga baya, mun fahimta cêwa kowanensu na da abin da ta kóyar da ʼyar uwanta. Gunjan ta taimaki Rachna wajen gani darraja rayuwa, ƙarin girman amana, da kuma koyon natsuwá da zumunci.

ADVERTISEMENT

Mahaifin Rachna-mai suna Dayal- ya na da horraren hali, da son íko. Yana hana ʼyan mata(Gujan da Rachna) daga yin rashin kunya, saduwa da ʼyan samari, da kuma sauran bidiyoyi na samartaka. Mahaifan Rachna-mai suna Shaul- ta na taimakawa wajen roƙon gafara wajen Dayal, da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin dangi.

Ku saurari tashan DStv Channel 166, ƙarfe bakwai na yamma, a ranar goma-sha-tara ga watan Oktoba, domin halárta wannan karo mai suna "Young Dreams".

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT