Pulse.ng logo
Go

Mai yayi zafi haka? 'Yar siyasa ta fallasa ma yar jarida mari don tana kama da mai tallar albasa

Lamarin ya faru ne a hedkwatar jam'iyar dake nan garin Accra yayin da yar jaridar mai suna Ohemaa Sakyiwaa, ta yunkura wajen daukar hoton yar siyasar.

  • Published:
Hajia Fati, yar siyasa da ta wanka wa yar jarida mari play

Hajia Fati, yar siyasa da ta wanka wa yar jarida mari

(Citinewsroom)

Wata yar gwagwarmayar jam'iya mai mulki na kasar Ghana ta NPP, mai suna Hajiya Fati ta fallasa ma wata yar jarida mari domin tana kama da mai siyar da albasa.

Lamarin ya faru ne a hedkwatar jam'iyar dake nan garin Accra yayin da yar jaridar mai suna Ohemaa Sakyiwaa, ta yunkura wajen daukar hoton yar siyasar.

Kamar yadda jaridar Citinews ta fita, a bayanin ita Hajia Fati, ta dauki matakin marin ta ne bisa tunanin cewa tana daya daga cikin magoya bayan tsohon mataimakin shugaban jam'iya wanda aka aka kora.

Tace tayi tunanin ta dauki hoton ta ne domin wata manufa daban kuma hakika "tana kama da mai tallar albasa, bata yi kama da yar jarida ba".

Rundunar yan sanda sun gurfanar da ita bisa laifin da ta aikata, tace za'a tuhume ta da laifin kai hari.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sanda yace za'a cigaba da bincike kan lamarin bayan karar da aka shigar.

Lamarin dai ya janyo tashin hankali a kasar musamman ga kafafen watsa labarai inda ake Allah wadai da faruwar hakan tare da neman adalci bisa lamarin.

Ita dai uwar jam'iya ta NPP ta nisanta kanta da lamarin inda tace a ko da yaushe zata cigaba da mara ma yan jarida baya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.